Friday, March 9, 2012

Ungulu Da Kan Zabuwa


Zai iya yiwuwa na yi rashin sa’ar tsundumawa cikin kogi mai mayunwatan kadoji, zarcewa cikin rijya mai masifaffiyar kasa ko fadawa kan kayar dake daji mai miyagun namun dawa.

Duk wannan tunanin na yi shi ne cikin ‘yan dakiku, rike da laima a dab da kofar jirgin, kafin na yi kundunbalar dirgowa daga jirgin don kubucewa daga mummunan hadarin da zai yi ba da jimawa ba.

Amma me? Addu’ar da na yi ta yi ta yi matukar tasiri, don kuwa lami-lafiya na sauka kan wani yashi dake cikin wani daji dake a gefen burtalin zuwa wani gari.

Kodayake dai na yi matukar farin ciki gami da godiya ga Allah dangane da saukata lafiya, amma ban tsawaita mamaki kan hakan ba. Abar da kawai ta tsawaita mamakina ita ce murya, wadda na ji a bayana, tana magana da harshen turanci, “Kamar a fim, amma na san gaske ne. Ka sauka lafiya?”

Na yi zumbur na juya yayin da mu ka yi tozali da mai maganar. Kyadildili ne mai gajeriyar faffadar fuska da mitsi-mitsin idanu. Ba na bukatar wasa kwakwalwata kafin na gane shi a matsayin mutum samfurin mutanen kasar Sin.

Na buda baki na amsa masa cikin harshen turancin, “Kwarai, kamar a mafarki. Na kuma gode. Zahiri na sauka lafiya.”

Ya gyada kansa, gyada kan da yanayinsa ya tuno mini da kadangare. Kana ya matso gare ni, ya miko mino hannu mu ka cafke, yayin da ya gabatar da kansa, “Sunana Wur Tsal.”

Na amsa masa, “Ni kuma nawa sunan shi ne Tukur Sarkin Yaki.”

“Sarkin Yaki?” Ya bida yana murmushi. “Ka ce ka zo garin da ya dace a lokacin da ya fi kowane dacewa.”

Na yamutse fuskata, “Ban ……..”

Ya katse ni ta hanyar daga mini hannu, “Jira mu karasa birnin Kussha. Za ka samu amsoshin duk tambayoyin da kake da su da kanka.” Kana zagaye ni, ya fara sassarfa ya nufi wani burtali. Sai da na dan yi jim, kafin na bi bayansa ni ma da sassarfar.

A lokacin da mu ka isa garin, mu ka kuma zagaya shi, sai mamakin dake zuciyata ya kara bunkasa, ganin cewa duk gidajen garin ba su da kofar shiga. Ban gane ma’anar hakan ba har sai, bayan da mu ka isa wani tafkeken dandalin da ya yi wa wani tafkeken gida kawanya. Tafkeken gidan ya zarta sauran gidajen garin ta fuskar tsayin katangar da ta zagaye gidan, ya kuma kamanci sauran gidajen garin ta fuskar rashin kofa. Akwai mutane maza da mata masu sifa irin ta Wur Tsal suna ta zarya a kofar gidan, shigen irin zaryar da ake yi a lokacin bikin sallah a kauye. Bambancin kawai shi ne, masu sayar da ababan makulashe a gurin duka abu guda suke sayarwa, wato kwanson kwakwa. Da na lura sai na ga masu sayen kwanson kwakwar a baki suke sakawa su kuma ci.

Wannan karon ban iya jurewa ba sai da na tambayi Wur Tsal, “Kwakuduba ce ta aure ku ne da baku da abinci sai kwanson kwakwa? Wannan ai sai ku raunana hakoranku.”

A nan Wur Tsal ya yi dariyar da ta nuna mini kwaftara-kwaftaran hakoransa, ya ce, “Dazu na ce maka ka zo garin da ya dace ne saboda sunanka sunan jarumai ne kuma garin nan ma garin jarumai ne. Mamallakin wannan tafkeken gidan da kake gani, mai suna Kussha, shi ne ya kafa garin nan. Kuma shi Kussha ya mutu ne a rana irin ta yau. Dalilin kenen da ya sanya duk rana irin ta yau ake irin wannan biki na baje kolin jarumta domin tunawa da irin jarumtar da ya nuna a rayuwarsa. Kuma tauna kwanson kwakwa a furzar da tukar na daya cikin bajimtoci biyu na wannan al’ada.”

Daganan sai ya je ya sayo kwanson kwakwar guda biyu. Tun ma kafin ya karaso gare ni ya balgaci kwanson ya fara taunawa, ji kake kurus. Da ya karaso sai ya miko mini daya daga cikin kwansunan, “Tauna don ……”

Na yi sauri na ce, “Azumi nake yi.”

A daidai wannan lokacin sai ga wasu mutane nan su biyar, kowane rike da kura, wadda aka sanya wa takunkumin baka. Dokacin kurayen sai muzurai suke yi kamar sa ci babu. Da na bukaci sanin abin da kurayen za su yi, sai Wur Tsal ya ce, “Kalaci.”

“Wane irin kalaci?”

Ya amsa, “Kalaci da wanda ba jarumi ba. Domin tun jiya rabon da a ba kurayen abinci. Nan ba da jimawa ba za a yaye masu takunkumin a kuma sake su. Muddin aka sake su kuwa, to mutanen gurin nan ba su da matsera sai gidan Kussha. Kowa can zai nufa, kuma, kai ma can ya kamata ka nufa.”

Cikin zakuwa na ce, “Ta yaya za a shiga gidan bayan ba shi da kofa?”

Wur Tsal ya ce, “Da kofa mana. Sai dai ba irin ta sauran garuruwa ba.”

“To a ina take, ya kai Wur Tsal?”

Ya ce, “Duk saman gidan ai kofa ce.”

Na daga kai na dubi doguwar katangar, kana na dawo da kaina gare shi, “To ai ban ga tsanin da za a tattaka don hawa katangar ba.”

Wur Tsal ya dube ni ya yi murmushi da zai ce, “Idan mutum shege ne shi a fagen jarumta to tashi kawai zai yi ya tsallake katangar ya dira cikin gidan. Kuma, shegantakar mutanen garin nan a kan jarumta take.”

A daidai lokacin da nake tunanin barin gurin tun da ni ba na tashi, sai aka yaye takunkumin kurayen nan, aka kuma sake su.”

Wane mutum! Ba sai mutanen gurin suka rinka tashi cikin gwaninta suna tsallake katangun gidan Kussha, suna shigewa cikin gidan ba! Cikin dan kankanen lokaci sai ya zama sai ni kadai na rage a gurin. Da dai na duba bayana da gefunana na kuma ga kurayen sun nufo ni baki bude, sai na yi kukan kura na nufi katangar. Da na kusa isa ga katangar, sai na rufe idanuwana, ina addu’a na daka uban tsalle. Amma ina! Addu’ata ba ta karbu ba, domin ko rubu’in katangar ban yi ba na ruguzo. Hakan kuwa ya kara wa kurayen kwarin gwiwar samun kalaci, don haka suka hanzarto. A lokacin da kurayen suka yi wo tashi za su dirar mini sai na kwalla ihun da ya zama mafarkin da ya farkar da ni daga barcin da nake yi.

Na yi zumbur na tashi zaune kan tattausar katifar, ina ta numfarfashi, yayin da garin ya yi tsit cikin talatainin dare. Daga nan sai na tashi na sauka daga kan gadon, na je na daura alwala, na yi nafila, kana na yi addu’o’i na kuma koma kan gadon da zummar kwanciya, amma ina! Maimakon haka sai tunanin mafarkin da na yi ya dawo mini, wanda hakan ya zama matursasin da ya tursasa ni alakanta manufar mafarkin da zahirin rayuwata.

Ni dai haifaffen birni ne gaba da baya, haka kuma ina cikin masu rufin asiri don daraktan mulki ne ni na wata karamar hukuma. Amma, da yake na fi sha’awar zama katoton bajimi a tsukakken garke fiye da zama madaidaicin bajimi cikin faffadan garken da manyan bajimai suka yi wa kaka-gida, sai na baro birnin na koma wata karamar hukuma da zama, inda bayan tsawon lokaci ina yi wa hakimin garin hidima sai bukatata ta biya, wato aka nada ni sarkin-yakin wannan karamar hukuma, domin babu taken da nake so a rinka zuga ni da shi kamar sarkin-yaki.

Anya kuwa wannan mafarkin ba manuni ne dake nuna mini cewa ina yin kwaina babu zakara ba? Kwai babu zakara mana, idan ba haka ba yaya za a yi na rinka amsa taken jarumin jarumai bayan buruntun bera ma firgita ni yake? In har ya zama wajibi in sarauci wani aiki mai ya sa wannan aiki ba zai dace da ni ba? Maimakon sarkin yaki, ya fi dacewa a kira ni da sarkin-yashe kudaden al’umma, tun da ni da ciyaman ne murguza-murguzan giwayen da ke kayar da baragen kason waccan karamar hukuma, a duk watan duniya. Anya kirana da sarkin-yaki bai zamo tamkar lullubar kura da fatar akuya ko yin ungulu da kan zabuwa don tabbatar tsarin nan na kashin dankali ba?

Amsa ta ga hakan ita ce, idan hakan gaskiya ne to ba ni kadai ya shafa ba. Domin kuwa, yawancin ‘yan siyasa kan yi karya da sunan talaka don kururuta mulkinsu, wasu cikin masu rawani da wasu cikin cikin masana addini kan yi amfani da sunan Allah da dadadan kalamai don martaba kansu, mawaka kan kambama manya don zakaka miyarsu, marubuta kan sanya batsa cikin rubutu don dabbaka kasuwar littafansu, da yawa cikin masu duba jarrabawa kan duba ta yadda suka so don bayar da dama ga ‘ya’yan masu kudi don su fi tabbata a mulkin al’umma ta hanyar tabbata a karatun jami’a ba. Anya ma ban taba jin wani mamallakin makarantar kudi yana cewa taimaka wa gwamnati suke yi wajen samar da nagartaccen ilmi ba, bayan shi kansa da dukkanin manyan kasar nan makarantun gwamnatin suka yi suka kuma zama abin da suka zama a yau ba? Hakika na ji shi. Abin da kawai bai ce ba shi ne samuwar makarantun nasu ne ke kara kassara makarantun gwamnatin da ‘ya’yan talakawa ke halarta ba. Anya ban taba sauraron wani masanin halayyar ‘yan Adam, wanda ya lissafo matsalolin zaluncin masu mulki kuma mirsisi ya ki cewa tsadanta karatu gami da toshe damar shigar ga wasu da kuma mugun nufi da yawancin mallaman , ciki har da shi, ke yi na sababin karuwar laifuffuka a kasar nan ba? Hakika na ji. Anya ma ban taba ganin wani talaka yana allawadai da irin zaluncin da shugabanni kan yi bayan shi ma yana zaluntar sauran talakawa ta hanyar zubar da shara a wajen gidansa ba tare da ya kone ta ba? Hakika na gani! Na ma ga talakan da yake sakin tumakansa kullum su fito, bayan ya san dabbobi na iya shiga gidan makwabcinsa su yi masa barna ba.

A nan sai zuciyata ta washe. A kalla dai ina da ‘yan uwa barjak, wadanda na fi wasu, wasu kuma suka fi ni kan waccan halayya ta takidin gina kai ko da kuwa za a danne na kasa.

Gamsuwa da cewa waccan mafarki nawa kamar fadakarwa ne gare ni ya sanya na tambayi kaina, shin ko na fadaku da fadakarwar wannan mafarki kuwa? Sanin da na yi na cewa naira naira ce ya sanya ni barin tambayar babu amsa. Har sai lokacin da kason karamar hukumar da nake wa darakta ya zo. Idan na iya jajircewa da cewa ban yarda a hada baki da ni a sace kudaden al’umma ba, na kuma iya dagewa da a sarrafa wannan kudi ta hanyoyi mafiya dacewa, to dole in girmama kaina. Idan kuwa na iya yin wani abu sabanin haka to mutuncina zai cigaba da zubewa a idanuwana saboda na taka rawa wajen nisanta maji kishirwa daga rafi zuwa kololuwar hamada.

1 comment: