Friday, March 9, 2012

Sai Da Ruwan Ciki

Ban kasance cikin jerin mutanen nan dake da halayyar kin tashi, har sai an tayar da su, sa’ilin duk da bangazau ya bangaje su ba. Na fi yarda da in kokarta mikewa da kaina don cigaba da halattacciyar rayuwata. Dalilin kenan da ya sanya na bijire wa dabi’ar nan ta sa’idanci, ta’addanci da bambadanci lokacin da na tsinci kaina cikin dimbin sallamammun ma’aikatan gwamnati a wani abu da ya fi kama da takidin kara talauta talautattu da kara bunkasa bunkasassu.

Bukatar cigaba da tsayawa kan siraran kafafuwana ta hadu da karancin hanyoyin samun kudi wajen haifar da hadowar hadirin talauci wanda ya tayar da guguwar gazawar da ta hargitsa kurar kuncin maraici gami da kadaicin da bai bar ni da wani zabi bayan yanke shawarar barin garin ba.

A ranar da na daure jakata na hau mota, abin da na sani shi ne birnin Kano na nufa amma abin da ban sani ba shi ne tafiyar wata aba ce da da na kasance boka to watakila da almutsutsaina sun tsegunta mini abin da zai biyo baya.

Kurnar Asabe ita ce unguwar da na sauka a birnin na Kano. Kasancewata bakon da ya je neman kudi gurin da bai san kowa kuma kowa bai san shi ba ya sanya ni fahihmta, a kasa da wata guda, cewa rashin samun aikin karfin da nake yi ya faru ne saboda dalilai biyu, wato rashin afkin jikina da kuma sifata ta ma’abota barci.

Da yake ban yarda akwai matsalar da ba ta da mawarwari ba sai na dau mataki kan waccan matsala. Matakin da na dauka ya zamo bin manyan kwatocin unguwar ina yashewa batare da kowa ya sanya ni ba. Manufata ta yin hakan ita ce la’alla ko hakan ya kawar da kallon rago da ake yi mini. Amma ina! Abin bai tafi yadda na so ba, don kuwa maimakon hakan ya kawar da wancan kallon da ake yi mini sai ya taimaka cikin dan kankanen lokaci abin ya tambara a unguwar cewa sabon mahaukaci ya bayyana.

Kallon mahukaci da aka rinka yi mini abu ne mai dakushe karfin gwiwa amma bai dakushe karfin gwiwata ba. Hasali ma wakar tsokana da yara suka rinka yi mini idan su ka hange ni ba ta taba sa wa na tanka masu ba. Tabbatar maganar nan ta masu hikima da suka ce Jigatar ruhi ne sirrin samun sahihiyar hikima sai hikimar waka ta rinka zuwar mini sa’ilin duk da nake cikin kwatamin. Ranar da ta zamo tauraruwar da ta haska wadancan kwanaki ita ce ranar wata asabar da safe. Ina dab da shiga wata kwata sai maigadin wani kayataccen gida ya zo ya ankarar da ni dangane da bukatar ganina da maigidansa ke yi. Don haka sai na bi bayansa har zuwa cikin gidan.

Mun iske maigidan a farfajiyar gidan tare da wata kyakkyawar budurwa, kowannensu na zaune kan farar kujerar roba. Bayan mun gaisa, sai mai gidan ya ce mini, “Sunana Dakta Abdu Nakowa. Wannan kuma,” Ya fada yana nuna budurwar, “’yata ce, Maryam. Kasancewarta dalibar jami’ar da aka uamrta da yin bincike kan wata cuta, wadda yanayinka ya sanya ta yi zaton cutar ta shafe ka, ya sanya ta son jin ra’ayoyinka kan wasu batutuwa. Idan ka yi mata kyautar lokacinka to za ka same ni cikakken mutumin dake yaba kyauta da tikwici.”

Da na waiwaye ta don jin abin da take son jin ra’ayin nawa kansa, sai ta fara da, “Abubuwan da kake yi sun sanya ka yin tambari a unguwar nan. Yayin da a bangare daya ka kan kaskantar da kanka wajen yin aikin da bai damu da lada ba, a daya bangaren kuwa halayyarka ga yaran dake tsokanarka ya sha bam-ban da yadda ya kyautu ka yi in har tsammanin da ake yi maka, na mahaukaci, gaskiya ne. Wannan ya sa ka yi mini kama da wanda ke da ruhin masu hankali da na masu rashin hankali duka a jiki daya.” Ta kura mini ido da za ta ce, “Ya kyautu kuwa in gamsu da hanyar da na bi wajen tunkararka a matsayin mafi sauki?”

“Na dauka ma ba za ki kare tambayarki da alamar tambaya ba,” Na fada ina mai nazarin dara-daran idanuwanta, “amma tun da an yi haka, amsata ita ce eh a’ah.”

Ta bida, “Me kake nufi?”

Na amsa, “Hanyar da ki ka bi tana da sauki amma ba ita ce mafi sauki ba. Hanya mafi sauki ita ce ta hanyar mamayar ruhin nan da bature ya kira hypnotism. Da kin yi amfani da wannan hanyar, da ki na dakinki ni kuma ina kwata, ruhinki zai mamayi nawa ki san duk abin da kike bukata daga gare ni ba tare da kin tsaya, gaba da gaba da ni ba. Hakan zai saukaka miki wajen yanke shawarar a ajin masu fama da tagwainiya (schizophrenia) da ya kamata ki sanya ni, a ajin paranoid ko na psychic?”

Wannan dan jawabin ne ya zamo mashimfidin da ya shimfida shimfidar gamsuwa da Maryam gami da mahaifinta suka yi cewa ban zamo cikin masu fama da cutar schizophrenia ba face takurarren mutumin da tsattsauran tarnakin da rashin sa’a ya yi mini ya sanya mutanen unguwar suka kasa fahimtata. Kuma ta dalilin haka Dakta Abdu ya yi mini alherin da ya ba ni damar zabar daya, cikin wakokin da na kirkira, wajen tace ta na kuma buga ta.

Wakar, mai baituka talatin, ta yi matukar karbuwa lokacin da na sake ta. Biyo bayan wakar farkon na fito da wasu mafiya ma’ana da dadin sauraro wadanda tabo mabambantan bangarorin rayuwa da suka yi ya sanya sunana ya karade kasar hausa cikin lokaci kankane.

Ban yi aune ba sai tsintar kaina na yi kan dokin farin jinin da ya rinka sukuwa da ni a fagen nasarar da, kasancewata cikinsa na tsawon shekaru ya ba ni damar kammala abubuwan da a baya na samu tawayarsu. Na yi auren da aka samu rabon jariri.

Ta dalilin tasirin da wakokina ke da su a harkokin al’umma ya sanya wata rana wani babban mutum ya bukaci ganawa da ni. Amma me? Manufar ganawar ita ce yi mini albishirin samun tsomuwa cikin kungiyar manyan kasa. A nan ya nuna mini wata takarda wadda ke dauke da sunayen mutane biyar, ciki har da sunana, wadanda suka yi sa’a aka shigar da su cikin wannan kungiya. Don haka rawar da zan rika takawa ita ce za a rinka ba ni abubuwan da ake so in rinka yin waka kansu domin cin nasarar kara ingiza al’umma zuwa inda ake so su ingizu. Inda ya kyasa mini cewa, baya ga tarin alfarmomi da za a rinka yi mana haka kuma za mu amfana daga janye tallafin shigowa da kayayyakin kasashen waje da gwamnati ke shirin yi.

Na taba yin mafrki an daga takobi za a sare mini kai. Da takobin ta taho gadan-gadan sai gabana ya yanke ya yi mummunar faduwa. Irin wannan faduwar gaban na ji lokacin da wancan babba ya gama jawabinsa.

Na dube shi, “Janye tallafin gwamnati daga kan abubuwan da ake shigowa da su kasar nan daga waje na fa nufin tashi da farashin komai zai yi a kasar nan. Hakan ai kamar kara jefa talaka cikin matsatsin rayuwa ne……”

Ya katse ni, “Matukar asirinka zai rufu me ruwanka da abin da zai shafi wani talaka. Kawai ka manta da wannan tsohon-yayin tunanin. Domin a yau muna cikin duniyar da gafiya ya kamata ta yi yadda duk za ta iya wajen tsira da na bakinta.”

Wannan batu nasa ya jefa ni cikin tunani. Wato duk da halin matsatsin da mafiya yawancin mutanen kasar nan ke ciki, wanda ya samu ta dalilin wawashe kudaden kasar nan da wasu tsirari ke yi, bai isa ba, shi ne aka bullo da wata hanyar ta kara takure su. Na zamo cikin tsirarin da za su amfana don kawai na cigaba da zama karen farautar masu son dawwama wajen dafe madafan iko!

Kodayake dai lokaci kan iya sauya komai amma na sha yin addu’a da kada Allah Ya kawo ranar da gatarina zai rasa abin sara baicin shuka. Domin, idan ban bai wa makaho sadaka ba bai kuwa kyautu in kwace sandansa ba. Wannan ce hujjata ta juya wa wancan kudiri baya. Juya bayan da, gudun kada in toni asiri, ya sanya suka tanada suka kuma sarrafa hujjojin karya wajen bayyana ni a matsayin cikakken mai aikata laifin karkashin kasar da kisa ne kadai hukuncina. Aka kuma tura ‘yan banga suka je gidana suka kone shi a matsayin hukuncin da mutane suka daukarwa kansu. Ta haka ran matata ya salwanta. Dan ne aka ci sa’a Allah Ya kubutar.

A lokacin da nake ta faman shan izaya a gidan kaso ne sai wata masoyiyar wakokina wadda ke da alakar nema tsakaninta da wancan babba. Ta yi shigar burtu, ta samo hujjojin da su ka karyata wadancan laifuka da ake tuhumata da shi, ta kuma gabatar da hujjojin a kotu. Kadayake dai daga baya ta rasa ranta, amma wata kakkarfar kungiyar duniya ta shigo lamarin, inda aka sake ni, aka kuma biya ni diyyar kazafi da kuma barnar da aka yi mini.

Tabbatar cewa gurbacewar duniya ya fi yadda na dauke shi tabarbarewa sai waccan kakkarfar kungiyar ta neme ni da su rinka amfani da ni ina munafurtar addinina. Fancakali da bukatar tasu da na yi ta sanya su ka kudiri aniyar dakusar da duk wani yunnkurin kara karfafa da zan yi. Wannan ya sanya na dauki dana na bar birnin Kano na koma gidan gonata dake kauyenmu.

Yanzu ne, da na kwantar da hankalina na samu damar fuskantar rayuwa. Ashe tarin kudi daban jin dadin rayuwa ma dabam. Ba kuma komai ke kara sanya jin dadin rayuwa ba illa kwanciyar hankalin da gamsuwar zuci ke bayar da shi.

Talakan da ya tsaftace zuciya da muhallinsa, ya kangare wa mutuwar zuciya da lalaci ya kuma fuskanci kansa, zai iya jin dadin rayuwa fiye da attajiri, mai mulki ko mallamin dake son ya fi kowa. Mutum bai isa ya fi kowa ba sai dai kawai ya taka rawar kidan da kaddararsa ta yi masa.

Hakika rashin kwantar da hankali ne sanadarin bata a rayuwa, kuma bayyanannen sakamakon ya kan zama ciwon zuciya ko kuma ciwon hauka. Kwantar da hankali kuwa shi ne ruwan cikin da sai da shi a kan janyo na rijiyar nasarar rayuwa.

Kuma, ga wannan gabar, ambaliyar kogin nazarin wani sashe na rayuwa ya kawo ni.

No comments:

Post a Comment