Friday, March 9, 2012

Tusa Ba Ta Hura Wuta

Ni dai mutum ne, kuma al’adar mutum ce ya yabi kansa kan wadansu abubuwa da yake tunanin ya kyautu a yaba masa, ya kuma gaza samun hakan. Don kuwa, baya ga idanuwana dake da saurin gane mutumin da na taba gani, ko da kuwa gani ne na dan kankanen lokaci, haka kuma kunnuwana ke da saurin shaida muryar mutumin duk da na taba hulda da shi.
Al’amarin da kan iya tabbatar wa da kowa cewa yabon kan nawa ya cancanta ya faru ne a hantsin wata lahadi, sa’ilin da nake hutawa da dunkufaffen kai, kan wani dakali wanda ke nesa da unguwarmu. Murya na ji ana yi mini sallama, kuma tun daga jin muryar kyakkyawar kwakwalwata ta shaida mini mai ita. Don haka da na dubi mai sallamar ban yi mamaki ba da idanuwana suka tabbatar mini cewa shi ne, wato talikin da ya taba shaida mini cewa sunansa Alaramman Fata. Mutumin da na yi la’akari da kallon fuskarsa wajen yin imanin cewa bai gane ni ba.
Kimanin shekaru shidda baya na taba tsintar kaina a kafe cikin lakar son samun kudi ba tare da wahala ba, duk kuwa da cewa sai na yi wahalar ya kamata a ce na samu. A wancan lokacin ne, yayin da nake dawowa daga Jami’ar Maiduguri, na hadu da wannan mutum, inda ya baiyana mini takensa ya kuma kalallame ni ya raba ni da kudaden hannuna, a madadin wata laya wadda ya gwada mini yadda ake yin kudi da ita. Ba mu jima da rabuwa ba kuwa na gane cewa damfara ta ya yi.
Na amsa masa sallamar, kana na fahimci batunsa. Ashe wai wannan ne zuwansa Kano karo na farko, kuma bai da wanda zai je gurinsa, ga kuma tsantsar yunwa da yake ji, dadin dadawa kuma bai da ko kwabo. Don haka ya kwantar da murya yake neman in taimake shi da abinci da kuma masauki.
Na ce, “Tabbata kai ni aka yi idan ka gan ni a Lahira.”
Ya ce, “Me ka ce?”
Na ce, “Cewa na yi wannan abar da ke hannunka ba waya ce mai tsada ba?”
Da ya amsa da ‘Eh’ sai na ce masa ni ma neman inda zan fadi in mutu nake yi. Don haka taimako daya da zan iya yi masa shi ne, zan raka shi inda zai fansar da wayar, da inda zai sayi abinci mai kyau. Maganar masauki kuwa ma yi ta bayan ya natsu. Da yake bai da wani zabi bayan hakan sai ya amince.

Mu ka je ya fansar da wayar kan kudi naira dubu goma, kana na raka shi kofar maciyar abinci ta Sterling Restaurant. A kofar maciyar na ce masa, “Nan ne inda za ka ci abinci a duk garin nan ka san ka ci, kai hasali ma turawan Ingila ne suka kafa gurin, kuma da sunan adadin kudinsu ake biyan kudin abincin.” Da ya tambaye ni dangane da tsada kuwa, sai na ce masa, “Ya danganta da yadda kake kallon tsadar. Bambancin shi ne ko ka san Abin da bahaushe ke cewa ‘fan daya’ Inda ya ce, ya sani.

Na kuma san zai ce ya sani din, don kuwa bahaushe kan kira naira biyu a matsayin fan daya.
Don haka sai na ce masa, “To abincin fam hamsin ma sai ka bar shi.”
Ya ce, “Ka ce ma duk abin rudu ne. Yo ko abincin hausawan zan ci ai na ci na naira dari.”
A wannan zaton nasa mu ka shiga, ya sa na sa aka kawo masa abincin fan hamsin. Bayan an kawo masa ya fara ci, sai na ce masa “Ka san abincin nawa kake ci kuwa?” Ya ce “Ba ka ce na naira dari ba ne?”

Na girgiza kai “Ni ban ce maka haka ba. Abin da na ce maka shi ne abincin fam hamsin kake ci, kuma duk fam daya na Ingila dai-dai yake da naira dari biyu da hamsin. Don haka abincin hamsin sau dari biyu da hamsin kake ci. Idan ka lissafa za ka ga abincin naira dubu goma sha biyu da dari biyar kake ci. Kuma kana da dubu gomar da ka jinginar da wayarka ka same ta, don haka idan ka gama za ka ba su dubu gomar, ya rage nasu su sa jami’an tsaron gidan su cukurkuda ka. Ka ga bayan ka fita sai ka cigaba da damfarar al'umma ta hanyar sayar masu da layar yin kudi.”
Kallon farko da ya yi mini ya tuno mini da kwantaccen dannannen ragon da ya hango mallamin yanka. Amma daga baya sai wancan kallon ya gushe, yayin da fuskarsa ta washe. Ya ce, “To fa! Wannan ramuwar gayya ce kenan. Sai dai na san a gare ni dama ba ta karewa. Kai ma kuma yana da kyau ka sani cewa ba kasafai tusa ke hura wuta ba.” Abu na gaba da na ga ya yi shi ne mikewa tsaye inda ya je gurin wani ma'aikacin gidan, bayan sun dan yi magana, sai ya koma tsakiyar dakin cin abincin ya yi gyaran murya ya ce, "To Jama'a, na shigo nan don cin abinci cikin rashin sani. Na dauka abincin fan hamsin na nufin biyan naira dari, sai bayan da aka zubo abincin na kuma fara ci sannan na gane fan hamsin din na nufin dubu goma sha biyu da dari biyar, kudin da ban taba mallakar adadinsu ba a rayuwata. Don haka nake son jama’a a taimaka a zo a taya ni ci in ya so sai mu yi karo-karo mu biya kudin. Amma ko ina da kudin, ni kadai ba zan iya cin abincin dubunnan nairori a lokaci guda ba.”

Hausawan gurin kuwa suka ce me za su yi in ba dariya ba? Hatta fararen fatun dake cin abinci a gun sai da suka rinka tambaya, da aka fassara masu abin da ya ce sai su ma suka rinka dariya. Ai nan take wani saurayi, wanda budurwar da yake tare da ita ke ta dariya, ya taso ya biya wa Alaramman fata kudin abincin. Kamar almara, a nan sai na ga mutane su na ta yi masa kyautar kudi. A nan na fice daga dakin cin abincin , na kuma bar gidan abincin.

Ko don rashin samun cikar buri ne ya sanya kwakwalwata dulmiya cikin tunani? Wato da ace burina na daukar fansa ya cika da tuni Alaramman fata na nan cikin wani mawuyacin hali. Abin tambayar shi ne me kasancewarsa cikin mawuyacin hali zai kare ni da shi? Ban dauki wani tsawon lokaci ba na gane cewa babu abin da zan karu da shi baicin gamsuwa. Irin gamsuwar dake hana sabuwar gwamnati dorawa kan aikin da tsohuwa ta fara matukar an samu sabani da jagororinta. Irin gamsuwar dake hana yin adalci tsakanin mutane biyu da suka samu sabani, wanda hakan yana matukar hana kasa cigaban da ya kamace ta. Mafita a nan ita ce a rinka rama naushi da rangwame maimakon a rinka rama shi da naushi.

Na dubi bakar kwaltar da motoci ke ta dawafi a kanta, kana na tuno da abin da Alaramman Fata ya taba fada, Tusa Ba Ta Hura Wuta! Kuma haka ne, domin da na kasance fasihi da na raka amshin wannan waka da daidaitattun baitoci,

Shi Jini Launinsa Ja,

Lauya Takamarsa Hujja,

Wanga tsari ya sa tusa

Ko Wuta Ba ta Hurawa

No comments:

Post a Comment