Tuesday, March 20, 2012

Dama Ba Ta Karewa

DAMA BA TA KAREWA

Ba kamar yau na gamu da babendaliyar budurwata, Halima ba, amma kamar yau na kama makwanci a unguwar Kofar Nassarawa da ke cikin birnin Kano . Kamar yau sa’idawan unguwar suka shaida mini cewa ban isa ba, bayan tun isa na da dadi na gama sanin cewa na isa. Haka kuma, kamar yau sa-toka-sa-katsin da har sai da ya yi sanadiyyar yayata al’amarin a kafofin yada labarai, ya afku, wanda ta sanadiyyar hakan har hukuma ta shiga al’amarin ta hanyar aika mini da takardar kira, wanda ga ni yanzu na amsa kiran.
Ko kusa ban yi mamaki ba da na iske cikin wadanda za su jagoranci ganawar har da manyan mallamai guda biyu, baya ga wakilan hukuma. Bayan sharar fagen zaman, sai jagoran zaman ya ce mini, “Labarin da muke da shi shine, ka zo da bakon abu, inda duk wayewar garin duniya wata mace, wadda ba ka da shaidar kasancewarta muharraamarka, kan je makwancinka, bisa ga amincewarka, ta dafa maka abinci, kana ta tafi. Tare da cewar mutanen unguwar sun sha nuna maka cewa hakan ya saba da koyarwar al’ada da addininsu.” Kana ya tambaye ni, “An yi haka?”
Cikin girmamawa na amsa da “Kwarai, an yi haka Ranka-ya-dade.”
“Kuma tunanin halin da za ka kasance ciki, idan tuburewarka ta fusatar da mutan unguwar har suka dau doka a hannunsu, bai taba shiga kwakwalwarka ba?”
Cikin girmamawa na kara amsawa da “Wannan tunanin ya shiga kwakwalwata tun ma kafin na tubure din, Ranka-ya-dade.”
“To mai ya sa ba ka bi doka ba don ka zauna lafiya?”
Na kaskan da murya, “Tare da girmamawa ga dokacin mutanen gurin nan, abin da na yi ni ban ga wani aibu a tattare da shi ba, baicin ta fuskar al’ada, wadda ba kasafai na fiye martaba ta kan al’amarin da baro-baro addini bai hore ni da guje masa ba. Ta yiwu karancin ilimin addini na damu na, amma abin da na san addini ya haramta shine kadaicewa ko mummunar cudanya tsakanin namiji da macen da ba muharramarsa ba. Idan aka dubi al’amarina da Halima ba za a iya cewa wancan hani ya shafe shi ba, don kuwa, Halima kan je masaukina da misalin goma na safe, sa’ilin da ba na dakin, ta dafa mini abinci, kana ta bar dakin bayan ta gama. Ba na ko tantama sanin da mutanen unguwar suka yi, na lokacin zuwa da tafiyarta, shine dalilin da ya sanya ba su dau doka a hannunsu ba. Amma abin da mutan unguwar ba su sani ba shine Halima na girka mini abinci ne don ni ban iya ba, gashi kuma sayen abinci kan iya tarwatsa bukatata ta adana wani abu cikin abin da nake samu, wanda ba shi da yawa. Kuma ina yin adanin ne don samun yadda zan yi in zama cikin yanayin da zan iya tunkarar kowane kalubale na aurar Halima. Don haka, bisa la’akari da bukatar aurar junanmu da muke da ita, gami da takurarren yanayin da muka zamo ciki, ya sanya muke yin abin da al’umma ke yi masa kallon rashin dacewa, maimakon taimaka mana da addu’ar Allah Ya cika mana buri. Wannan shine dalilina, amma na yi alkawarin idan mallaman dake wurin nan suka ga rashin dacewar yin hakan, to daga yau zan daina.”
Daya daga cikin mallaman ya dubi jagoran zaman ya ce, “Ina ganin idan da yadda hukuma za ta yi ta taimaka wa wannan bawan Allah wajen cimma burinsa, to ya kyautu.”
Haka kuwa aka yi. Hukuma ta saya mini gida, ta bani jari, ta kuma jagoranci daurin aurena cikin abin da ya gaza wata guda. A ranar da na shiga cikin dakin matata dake cikin sabon gidana na iske Halima, bayan mun kintsa kanmu, sai ta ce mini, “Har yanzu fa mamakin yadda aka yi har ka samu wannan damar nake yi.”
Na ce “To ki daina. Don tare da cewa duniya na fama da mashasshara, amma damammakin dake cikinta ba sa karewa, matukar dai anyi katarin iya amfani da mashassharar wajen yin sara kan gaba.”
AN KARANTA AN TACE A RANAR LAHDI 05/07/2009 YAYIN TARON ANA

No comments:

Post a Comment