Friday, March 9, 2012

Bakin Dare

Sai bayan gotawar karfe daya da rabi na dare batare da alamun karfin jikin da nake ji ya soma raguwa ba, illa iyaka ma karuwa da yake, sannan na ankara cewa ta yiwu babu ni a cikin wadanda ke da rabon yin barci a daren.

Gashi dai kwakwalwata na matukar bukatar hutu amma idanuwana tangararau. Jikina kuwa ji nake kamar yana tsikari na saboda tsantsar kwarin jikin da nake ji yana kara mamaya ta. Na yi kwafa na cillar da littafin da na jima ina dubawa, kana na mike zaune. Shin mene ne dalilin da ya sanya daren na yau ya bambanta da sauran a gare ni?

Bayan ninkayar da na yi ta yi cikin kogin tunani sai na gano cewa hakan ba zai rasa nasaba da shayin da na sha a farkon daren na yau ba. Shayin da dandanonsa gami da gurin sayar da shi ya sha bamban da na saura.

A lokacin da karfe biyun dare ta gota sai na ji ba zan iya cigaba da zama cikin daki ba, don haka na mike, na bude kofar shagona kana na fito waje. Na kalli dogon layin, wanda farin wata ya matukar rayawa da dan karen hasken da duk da matsalar rashin wutar lantarki amma ban samu matsala wajen gano aibun layin ba. Babu shakka, babban aibun faffadan kwararon shi ne rashin lambatu. Don haka mai zai hana na yi kishin kasa na haka lambatun cikin daren ta yadda sai dai mutanen unguwa kawai su wayi gari da aikin da na yi? Ta yiwu ma jin dadin aikin lambatun ya sanya a ba ni mai-unguwar unguwar duk kuwa da kasancewata ba zuwe a unguwar.

Sai dai me? Haka ba ya taba yiwuwa da yatsun hannu wadanda su kadai ke gare ni a ababan da za a iya aiki da su. Wannan ya sanya ni tunanin inda zan samu magirbi da diga da shebur wadanda da su ne kadai aiki irin wannan yake yiwuwa. Shin ina zan same su?

Kamar amsa ga wannan tambaya tawa sai cikina ya kada, alamar dake ishara da bukatar yin juyen bahaya nan ba da jimawa ba. Don haka na kama hanya na nufi dakina wanda cikinsa ne bandakina yake. Sai da na je dab da shiga sai na ja na tsaya. Me zai hana na tunkari bola don yin juyen bahayan? Domin idan na ci sa’a ma na iya yin tsintuwar kayayyakin aikin da la’alla wani birkila ya manta. In na yi wannan sa’ar kuwa to na kashe tsintsaye biyu kenan da dutse guda.

Wannan ya sanya na juya na nufi hanyar da za ta kai ni bolar dake bayan gidan Alhaji Bello Matsolo. Haka na yi ta tafiya har na isa karshen kwararon, kana na mike kwaroron da bolar da na nufa take. A lokacin da na isa kofar gidan Alhaji Bello Matsolo tuni har bahayan da nake ji ya matso ni, don haka da sassarfa na karasa bolar na kuma shiga ciki ina tunanin inda ya fi kamata na juye bahayan. Kallo daya na yi wa bolar na hango wani abu tullulu mai kama da kifaffen tulu, don haka sai na karasa gurin na sa kafa da zummar buda shi.

Abubuwa biyu ne suka sa bahayan da nake matukar ji ya bace bat. Na farko dai, da kafata ta shuri abin sai na ji shi lagwaigwai, alamar da ta tabbatar mini cewa abu mai rai na shura. Na biyu kuwa shi ne gwauron numfashi da abin ya yi, kana a hankali sai na ga wani abu a gefena ya motsa. Da na lura sosai sai na ga abin ashe hannu ne ya yaye wasu tsummokara dake kusa da ni sa’ilin da kan abin ya bayyana, kana ya mike tsaye cikin zafin nama ya dube ni.

Da ban kasance cikin tsantsar rudani ba da hakika na tintsire da dariya. Abin, mai sifar mutane, bai yi mini kama da komai ba in ban da shirgicecen mutum mai tullukeken ciki kamar randa. Dadin-dadawa kuma, ba ya sanye da komai a jikinsa in ban da wani bujukuran gajeren wando. Amma ina! Haka nan na daskare a tsaye ina jiran ya yiwo kaina ya halaka ni.

Maimakon hakan sai na ga ya juya da gudu ya bi ta cikin bolar har ya je karshenta, inda daga nan sai ya bulle ta daya kwararon ya yi tafiyarsa. Bayan shudewar wasu ‘yan dakiku sai na dawo hayyacina. A rude na fito daga bolar bisa ga burina na komawa shagona. Amma da yake a rude nake, sai na kara nitsa cikin kwararon maimakon in fita daga shi.

Can sai na hango hasken fitilar da na yi zaton na mota ne, don haka sai na rage gudu ga zatona na cewa wani Alhajin ne ya yi dare. Ta yiwu idan na yi masa bayani ya taimaka ya rage mini hanya zuwa dakina. Da motar ta karaso, na tsayarta sai ta tsaya. Don haka sai na karasa kofar direba. Ina dab da fara yi masa jawabi sai ji na yi an damke ni ta baya. Na yi kokarin kwacewa amma ina! Wanda ya damke nin ya fi ni karfi, nesa ba kusa ba. Kana sai na ji wata kakkaurar murya na yin magana a barin kunnena na dama.

“Kada ka bata lokacinka, samari,” muryar ta cigaba da fadin, “Don kuwa ba za ka iya kwacewa ba. Ta yiwu idan kana da dogon kwana ka kwace a can gurin yanka, amma ba daga hannuna ba.”

Hakan da kuma kamshin turaren dake tashi daga jikinsu ya tabbatar mini cewa ‘yan mafiya ne. A karo na biyu, tun bayan fitowata daga dakina, sai kwakwalwata ta kara tsayawa. Ba ta tashi cigaba da aiki ba sai da na ji direban motar na cewa wanda ya rike ni, “Sake shi Baba, ba mutum ba ne. Dubi karshen inda hasken fitilar motar nan ke haskawa. Ga dan’uwansa can yana tahowa.”

Ban tashi gane abin dake faruwa ba sai bayan da na ji an sake ni, na kuma kalli gaban motar na hango halittar nan da na taso a bola. Sai yanzu, da fitilar mota ta haske shi sannan na ga ashe kurtsetsen cikin nasa launin toka ne kamar yadda fuskarsa ma ta zamo hakan. Da da rana kuma cikin jama’a aka gan shi sai a yi zaton tashe zai je.

Tun kafin motar ta gama yin ribas na fita da gudu. Na bi ta wani lungu kana na sha kwana. Shan kwanar tawa da wuya kuwa sai na ji na taka wani abu mai laushi, wanda daga baya na gane ashe cikin masifaffen kare na taka. Na gane haka ne ta hanyar jin haushin da karen ya rinka yi sa’ilin da ya biyo ni ya kuma rinka hankoron cafar agarata. Wannan ya sa na kara gudu kamar raina zai fita. Har na isa layin Bello Matsolo karen bai daina bi na ba ni ma kuma ban daina gudun ba. Hasali ma ta kasan wata bishiya na huce, bishiyar da ake tsoron tunkararta saboda tarin kudan zuman dake kanta. Ina karya kwana kuwa sai karen ya dako wani uban tsalle ya dira a gadon bayana, hakan ya sanya na fadi na yi rub-da-ciki. Cikin zafin nama, karen ya mirgine ya kara yi wo tsallen da babu tantama sai ya turmushe ni. A sannan ne na ji wata kara a lokaci guda kuma na ga wani haske mai kama da walkiya. Maimakon karen ya turmushe ni, sai ya fadi gefe guda ya mimmike.

Ban yi azarbabin yin ajiyar zuciyar kubuta ba har sai da na fara kallon inda hasken ya fito. Gabana ya yanke ya yi mummunar faduwa da na hango mutanen da yawansu ya kai biyar, kowannensu rike da bindiga. Ba na bukatar wasa kwakwalwata kafin na gane mutanen a matsayin ‘yan fashi da makami.

Ban san lokacin da na yi kukan kura na mike tsaye, kana na juya da baya na bi hanyar da na biyo ba. Ina karya kwanar kuwa sai na ji karar tagwan harsasai da suka harbo. Da dai ban ji wani abu ya shiga jikina ba sai kawai na cigaba da gudun da nake, yayin da na ji takun sawayen wasu cikinsu sun dafo mini baya. Wannan ya sanya na kara dagewa bisa ga aniyata ta kai wa mararraba don kara karya wata kwanar. Amma abin bai tafi yadda na so ba, domin kuwa ina karya kwanar sai na yi karo da wani kakkarfan abu, wanda, saboda tsantsar gudun da nake yi sai da muka fadi tare da shi. Na hanzarta mirginewa na dube shi na kuma gane shi a matsayin mai kurtsetsen cikin abin nan da na taso shi a bola. Bambancin kawai shi ne wannan karon sai ya yiwo kaina ya turmushe ni, da na yi yunkurin yin kara sai ya sa wani abu mai kama da hannu ya rufe mini baki. Kana ya yi mini magana cikin rada, “Kada ka mike tsaye. Barayin da suka biyo ka gidana suka je. Ni ne Alhaji Bello. Kada ka yi motsi. Kwanta kawai abinka. An ce idan mutum na da hakuri akasarin matsalolinsa kan warware kansu da kansu.”

Na kuma kwanta na kuma yi shiru amma ba don na gamsu da shawararsa ba, sai don ba yadda zan yi. Ai kuwa sai na ji karaji da hayaniya gami da tarwatsewar mutanen da na tabbatar su suka biyo ni. Bayan dauwama da karajin ya yi na tsawon wasu dakiku sai mu ka ji shiru.

Sai daga baya na gane abin da ya faru. Ashe harsasan nan da ‘yan fashin suka harbo mini ne suka zarce kan bishiyar nan da kudajen zuma ke kanta, suka kuma tarwatsa kudajen zuman suka yo kasa, wanda cikin rashin sanin abin da suka yi, ‘yan fashin suka karaso da niyyar hucewa inda haushin kazar kudajen zuman ya huce kan ‘yan fashin.

Haka kuma ashe wannan kurtsetsen mutumin ya yi gaskiya da ya gabatar mini da sunansa a matsayin Alhaji Bello, wato Bello matsolo. Ashe ‘yan fashin gidansa suka je, inda ya ci sa’a ya hange su tun kafin ma su shiga gidansa. Kasancewar dokacin iyalansa sun yi tafiya, sai ya baro gidan, ya kuma yi bad-da-bami ta hanyar bursune jikinsa da toka ya kuma saje da tarkacen bola, inda a can na fara ganinsa cikin wannan dare.

Dadin dadawa, ashe ya ji karar harbin da ‘yan fashin suka yo mini, ya kuma yi zaton inda harbin zai je da abin da zai haifar. Wannan ya sanya shi ya rike ni gudun kada fantsamar kudajen zuman ta shafe ni

Duk na san haka ne daga baya, lokacin da bayan gushewar karajin ‘yan fashin, Alhaji Bello ya tashe ni, muka hanga kwararon inda muka hango gabadayan ‘yan fashin a kwankwance a kasan bishiyar.

Sai yanzu da na tabbata na yi cikakkiyar kubuta sannan na gane cewa hakika Alhaji Bello Matsolo ya yi dai-dai da ya ce, matsalolin mutum na iya warware kansu matukar mutum ya yi hakuri a rayuwa. Abin da kawai Alhaji Bello bai ce ba shi ne matukar mutum na da gaskiya. Tabbas tsanani ba ya dorewa matukar dai mutum bai bari tsananin ya karyar masa da zuciya har ya yanke kauna daga rahamar Ubangiji mai kowa mai komi ba. Ga mamakina sai na samu cewa na matukar amfanuwa daga bala’in da na shiga cikin wannan dare. Shin dama haka ne da masu hikima suka ce shiga taskun rayuwa na taimaka wa mutum wajen samun sahihiyar hikima? Idan ko haka ne, shin na yi adalci kuwa idan na kira wannan dare da bakin dare?

No comments:

Post a Comment