Friday, March 9, 2012

Hudubar Shaidan

Hamisu ya yi tsaki ‘Mts.’

Ya yi tsakin ne bayan da ya kwashe tsawon wani lokaci yana kokarin tayar da jannareton wanda mirsisi ya ki tashi. Wani abin da ya kara kwarara fetur ga wutar bacin ran na Hamisu shi ne da karbo jannareton daga gurin gyaran, da ya haura sati guda, ba a fi sa’o’i biyu ba. Ga kuma tarin aiyukan mutane da suka haura mako guda a gurinsa, aiyukan da ba sa yiwuwa sai da wutar lantarkin da rashinta ya sanya ko taba aiki daya cikin tarin aiyukan da ya karba bai yi ba, tare da cewa tuni kudaden aiyukan da ya karba sun zama radaddu.

Sabi’u, wanda ke kallon duk ficikon da Hamisu ke yi da kagaggiyar zuciyar rashin samun aikinsa akan kari, ya ce, “Allah wadaran nasara. Ya rasa abin da zai yi sai abin dake bakanta wa al’umma rai.”

Hamisu ya nuna igigyar jannareton , ya ce, “Ita ma wannan shegiyar gajeriyar igiyar da laifinta.” Kana ya dubi Sabi’u, “Ko za ka zama igiya ne , in kara ka da ita, in gani ko hakan zai sanya injin tashi?”

Sabi’u ya yi shiru bai ce uffan ba. Kuma rashin cewa uffan din har cikin zuciyarsa. Yaya za a yi Hamisu ya shigo da maganar wasa cikin abin da ka iya janyo masa maimaita shekarar karshe ta karatunsa na jami’a? Wannan ya sanya ya dauke kansa daga kallon Hamisun. Hakan ya hana Sabi’u lura da lokacin da Hamisun ya koma ya shige cikin shagonsa. Lokacin da Sabi’u ya lura da Hamisun shi ne sa’ilin da ya fito daga shagon, rike da wata igiyar, wadda a ido ta fi waccan alamun kwari. Yanayin yadda Hamisun ya taho ya tuno wa Sabi’u da wani kakkarfan jarumin Hindu, sa’ilin da yake shirin tunkarar mugu, ta yadda da Sabi’un ya zamo cikin nishadi da ya yi wa Hamisu irin taken da aka rinka yi wa wancan jarumi wato daran-daran-daran.

Lokacin da Hamisu ya isa ga injin sai ya nannada igiyar kan matayar da injin yana muzurai, kana ya takarkare ya ja igiyar da karfin da ya sanya igiyar tsinkewa. Hamisu bai yi aune ba sai ji ya yi ya yi baya ya kuma fada kan Sabi’u, kana gaba-dayansu suka doku da garu. Kan Sabi’u ya kume a jikin garu, ji kake kuum!

Haushi ya kara turnike Sabi’u, ya yi shiru ya kasa magana har sai da Hamisun ya samu ya matsa daga jikin Sabi’u. Hamisu ya dubi guntuwar igiyar dake hannunsa, ya ce, “Wai da nasara ya kera jannareto, uban waye ya hana shi yin remote control a matsayin abin tashinsa?”

“Ina jin ubanka ne.” Sabi’u ya amsa.

“Kuturu!” Hamisu ya fada a harzuke, “Ka zage ni?”

Sabi’u ya amsa yana ciccije baki, “An zage ka din. Aiki fa na kawo maka, ba kwangilar wulakanta ni ba.”

Hamisu ya ce, “Ka ga kuwa, da ba ka kasance a kofar shagona, kada na cukurkuda ka a zarge ni da ragwanci ba, da jikinka ya gaya maka.”

Sabi’u ya ce, “Kana ganin cinta kenan!”

“Da shanta, da hadiyarta kai har ma da kasayarta ina gani.” Inji Hamisu.

Sabi’u ya ce, “To idan ka cika shege ka biyo ni.” Kana ya juya ya nufi bakin titi a kufule, yayin da Hamisu ya bi bayansa, shi ma a kufule. Da yake tuni har karfe taran dare ta gota, sai da suka yi jira na kusan mintunan rubu’in sa’a kafin su samu babur. Dan acabar da suka samu shi ma matashi ne kamar su. Ya tambaye su, “Ina zuwa?”

Sabi’u ya amsa, “Duk inda ka san za mu iya raba raini da wannan tsamin.” Ya fada yana nuna Hamisu.

Dan acabar ya nazarce su kafin ya ce, “Casuwa za ku je yi kenan.”

Hamisu ya ce, “Ai ka san su kananan shegu sai ana raba raini da su.”

Dan acabar ya ce, “Da kyau. Dama ban samu damar kallon damben dazu ba. Don haka, kyauta ma zan kai ku. Ku dai ku hau.”

Suka kuma hau. Hawan da bayan tuki na tsawon lokaci suka isa wani guri wanda ya cika dukkanin sharuddan gurin da suke nema. Dan acabar ya yi fakin yayin da suka sauka. Hamisu da Sabi’u suka shata da’ira amma kafin su fara abin da ya kawo su sai dan acabar ya ce, “kafin fara kallon fadan, zan so sanin dalilin fadan idan da hali.”

Sabi’u ya nuna Hamisu, “Laifinsa ne…”

Dan acabar ya dakatar shi, “Dalilin kawai nake son sani.”

Suka buda masa hoto mai kala na al’amarin da ya janyo rikicin nasu. Dan acabar ya ce, “To ai wannan dalilin bai kai ku ji haushin juna kansa ba. In har za ku ji haushin wani to haushin wandanda alhakin bayar da wutar lantarki ya rataya a kansu ya kamata ku ji.”

Wannan lafazin ne madigin da ya diga ayar karshe dangane da batun raba-rainin da Hamisu da Sabi’u ke shirin yi. Hamisu ya dubi Sabi’u, “Haka ne fa Sabi’u, haushin kazar rashin cikar burinka bai kamata ya huce kan damin raunina ba.”

Hamisu ya ce, “Ko dai kana nufin ka ce naka raunin bai kyautu ya kullaci nawa ba.” Kana gabadayansu suka tintsire da dariyar da a karshenta Sabi’u ya ce, “Gaskiya duk ranar da duk na samu wata dama ta mulkar al’umma to ya zama wajibi in huce haushina. Don wallahi cinye-du zan zama.”

Sabi’u ya ce, “Kai dai bari in kammala digirin in samu wata dama. Sai na warci duk abin da zan iya na kowane irin kudi da zai gilma ta kasan tebirina. Ni kam wartau zan zama.”

Dan acabar, wanda ke sauraronsu, ya yi ajiyar zuciya, “Ai na yi tsammanin rashin adalcin da ya shafe ku zai karfafa maku gwiwa ne wajen ganin guje shi, sa’ilin duk da ku ka samu dama, la’alla ko na kasanku sa taso da kishin kasa na hakika.”

Hamisu ya ce, “To kana kuwa bukatar sake tsammani. Domin babu abin da zai sanya ni sauya wannan niyya tawa.”

Sabi’u ya ce, “To ai ni, tun da na kusa gama shan tawa wahalar, ba ma na so a samu sauyi wajen tafiyar da jagorancin al’umma. Kasa ma ta fi dadi ga bunkasasshe idan ba a martaba doka, kuma talauci da alfarma suka yi yawa.”

A nan sai dan acabar ya ce, “Ashe zuciyoyinku ne suka gurbata shi ya sa ku ka dace da shugabanni. Kuma na yi imanin haka zuciyoyin akasarinku suka gurbata. Ku kuma rike wannan cikin zuciyarku cewa sai kun yi nadama.”

Hamisu da Sabi’u suka bushe da dariyar da ba ta tsawaita ba. Wannan ya faru ne kuwa saboda bacewa da dan acabar gami da baburinsa suka yi. Ai nan take idanuwansu suka raina fata. Ashe baburin aljani suka hawo. Kuma kowannensu ya koma gida ne a tsure, kamar yadda kowanensu ya sanar da mutan gidansu abin da ya faru. Babban abin da ya fi damun kowannensu shi ne furucin dan acabar na karshe. Wannan ya haifar da gamuwar da mahaifansu suka yi, inda suka yi shawarwari, daga karshe suka samo mafita, wato kai kuka zuwa gurin mallam Batarsu.

Suka kuwa je gidan mallam Batarsu, wanda ke a wani kungurmin kauye. Sun iske wata kyakkyawar budurwa a farfajiyar maganar mallam, wadda da ita suka yi jira har mallam ya fito. Mallam Batarsu ya yi umarnin cewa gabadayansu su shiga, don haka da budurwar, da Hamisu da kuma Sabi’u suka fuskanci mallam, wanda ya fara magana, “Na yanke shawarar ganinku a lokaci guda ne saboda al’amuran da suka kawo ku suna da kamanceceniya.” Kana ya dubi budurwar da zai ce, “Ke kin zo ne saboda neman tallafin gano inda bataccen mahaifinki yake. Hakika mahaifinki na nan da ransa, kodayake dai yana cikin wani mawuyacin hali, kuma dab yake da rasa ransa. Kuma, yin sanadin kubutarsa daga wadanda suka kama shi kankanen abu ne a gare ni. Sai dai ba zan taimaka wajen fitowarsa ba ko nawa za a bani. Dalilina shi ne, gaskiyar mahaifinki ta yi yawan da nan gaba zai iya hure wa talakawa kunne su yi bore, ni kuma ba na son haka. Domin, idan yanayin bai zamo cukurkudadde ba to mutane irin mu ba za su samu kulawa daga gurin manya ba domin sana’armu ba za ta yi tasiri ba. Su kuwa, wadanda suka kama shi sun yi haka ne domin yin amfani da sassan jikinsa wajen yin wani asiri, wanda ba zai yiwu ba sai da sassan jikin mutumin kirki. Don haka nake ba ki shawara da ki dauka cewa rashin mahaifinki kamar wata hadaya ce da aka yi don kyautata rayuwar mutanen da suke da ra’ayin amfanuwa da sana’armu.”

Budurwar ta dube shi, “Ai ban san haka kake ba, da ban zo ba. Kamar yadda ka ce, za ka iya taimaka mini amma ba za ka yi ba, to ko da cewa ka yi za ka taimaka mini a kyauta ba zan karbi taimakonka ba. Na gwammace wa rasa komai da na karbi taimakon mugu.” Kana ta tashi a fusace ta fice.

Mallam Batarsu ya dubi su Hamisu ya ce, “Idan na so zan iya jifan ta da jafa’in da ka iya lahanta rayuwarta. Sai dai ba zan yi hakan ba kawai don ba ta yi wa mahaifinta irin gadon da albasa ta yi wa ruwa ba. Kuma kamar yadda nake son gurbatattu su yawaita a kasa, haka ma ba na fatan a nemi mutumin kirki a rasa a kasa, domin lokaci zuwa lokaci aiki kan taso mana wanda lallai sai da sassan jikin mutumin kirki yake yiwuwa.” Kana ya yi murmushi, “Ku kuma, tsoron da kuke ji na barazanar da karamin aljanin nan ya yi maku, ku daina shi. Irin ku na fi so ku yawaita a kasa. Yau din nan zan umarci Tuburzuku ya kamo mini karamin aljanin, da ya tsorata mini ku, ya daure mini shi a gidana. Daga yau ya daina yawo, ballantana har ya samu damar kara tsorata mini masoya irin ku.”

Sabi’u ya tambaya, “Ran mallam ya dade, wane ne kuma Tuburzuku?”

Mallam Batarsu ya bushe da dariya, “Ba ka san Tuburzuku ba, ko? Ai shi ne ke cin zalin aljanu ya kuma zauna daidai. Ka ga kuwa shi ya iya jan zare, ba jan-zare ba.”

No comments:

Post a Comment