Friday, March 9, 2012

Tarwatsewar Mafarki

Ba gargadi, ba zato ba kuma tsammani sai motar dake gabana ta tsaya cak a tsakiyar titin. Wannan ya sanya take birki cikin gaggawa da na yi ya yi rashin nasara ya kuma zama sular nasara. Rashin nasara wajen kasa hana gaban motata bugar bayan motar dake a gaban nawa, kamar yadda sular nasarar ta zamo bayar da dama ga gaban motar dake bayana ta bugi bayan motar tawa.

Batare da yunkurin gefencewa ba, sai, ganin direban motar gaban nawa ya fito, ni ma na fito yayin da direban motar bayana shi ma ya fito.

Da yake direban motar gaban nawa ne ya haifar da buge-bugen motocin, sai na yi zaton uzuri zai kawo, wanda da hakan ya yi da na ce masa kada ya damu mu fara gefencewa tukunna. Maimakon hakan sai kawai ya bangaje ni, ya fara aibanta tukina yana cewa shi ma’aikacin hukumar kare hadura ne, kuma shi bai taba fara barin filin daga ba don haka sai ya nuna mini kuskurena.

Ba kuma mamaki, tsoro ko takaici ne ya sanya ni yin shiru, na zuba wa sarautar Allah idanu ba, a’a, yakini da nake da shi ne na cewa, kamar dai yadda hargowa ke nuni da raunin guguwa, haka shi ma shiru ke nuni da karfin dutse. Kuma, ko su masu fara barin fagen dagar ai barin kamar zilliya ce wadda ta kasance salon yaki wanda shi kuma dan zamba ne kamar yadda Lincoln da Sun Tzu suka bayyana. Kamar yadda sayyidna Mu’awiyya ya bayyana. Haka kuma kamar yadda shi shugaban halittar kansa ya baiyana.

Direban da ya buga mini, tare da wasu da suka ga gaskiyar abin da ya faru suka rinka ba ni baki, suka kuma gargadi shi wanda ya fara bugawar da cewa, matukar ya cigaba da kokarinsa na aibanta ni to kuwa a shirye suke da zuwa ko ina ne wajen ganin sun shaide ni. Da dai ya ga babu sarki sai Allah sai ya yi kwafa ya tafi. Kana suka kara ba ni hakuri, inda na gode masu dangane da kasancewarsu mutanen kirki.

Bayan komai ya lafa na shiga motata na bar gurin, sai kirkin wadannan mutane ya rika bijiro mini. Na tuna da yadda suka kashe wutar da kuma yadda suka yi ta ba ni baki. Da sun san ni da sun san cewa kashe wutar kawai da suka yi ma ya wadatar, da ba su dage da ba ni hakuri kan na kyale mutum da aniyarsa don samun maslaha domin kuwa murhun garwashin wutata ya yi sanyi.

Murhun garwashin wutata ya yi sanyi!

A wani yammaci, lokacin kuruciyata, an yi iska mai matukar karfin da har ta rakakkabo jemagun dake kan wata bishiyar dabino dake a gewayen gidanmu. A wancan lokaci, farin cikin da mu ka yi, ni da abokina Sanusi, shigen irin wanda makalaci kan yi ne sa’ilin da ya tsinci dami a kalansa. Ba mu yi wata-wata ba muka tattara wadancan jemagu cikin wani buhu, kana muka tunkari gidan mista Tunde bisa ga tunaninmu na sayar masa da jemagun, tun da an taba shaida mana cewa bayerabe ya samu jemage kamar mu ne mu samu naman kaza.

A kan hanyarmu ta zuwa gidan mista Tunde muka rinka tattauna yadda kowannenmu zai yi da nasa kason kudin jemagun. Yayin da Sanusi ke da burin sayo kura don ya rinka sanya ta tana cinye duk wadanda ke cin zalinsa a makaranta, ni burina ga kudin bai huce sayo giwa ba. Giwa mana, wadda zan boye ta har sai ranar hawan Nassarawa in hawo abata. Sauran mutane a kasa, wasu a kan dawakai, ni kuma akan giwa! Dole a kalle ni.

Amma al’amarin bai tafi yadda muka zata ba. Da muka kai wa mista Tunde jemagun muka kuma shaida masa dalilin kai masa jemagun, maimakon hakan ya burge shi, ina! Sai ya tunzura ya biyo mu da duka yana korafin wai mun raina masa wayo. Da kyar dai kafarmu ta kwace mu a waccan rana.

Har kullum na kan lura da wancan al’amari a matsayin notin da rayuwata ta rinka juyawa kansa. Tunanin hawa giwa lokacin hawan sallah tunani ne dake nuna tsantsar tasirantuwa da karfin iko gami da tsananin bukatar fin karfin kowa da komai. Kodayake dai, shan bamban da al’amarin ya yi da tsammaninmu a wancan lokaci ya sanya na ji a jikina cewa na rasa wani abu amma ko kusa rashin bai dakushe mini karfin gwiwa ba. Na cigaba da kai-kawo wajen ganin na cimma babban matsayin da babu kamarsa. Ta haka na zurfafa a karatun bokon da har na zama furofesa. A wancan yunkuri, na je manyan birane na manyan kasashen duniya da dama.

A wasu kasashen na ga kishin kasa na gaske, wanda mu ka rasa ga shugabannin kasar nan, amma ban ga kwanciyar hankalin shugabanni ba. Na ga kimanta alkawari da bin doka amma ban gano watayawa ba. Na gano tausaya wa ‘yan kasa maras sa karfi amma ban gano alfarma ga malalaci ba. Na ga tasirin sahihanci amma ban gano ingancin rudu ba. Na jiyo kamshin abinci amma ban ji daidaitaccen dandanonsa ba. Tirkashi! Kusan a duk inda na gano wani abu mai matukar muhimmanci da muka rasa a kasarmu, na kan hango wani amfanu da rashin nasa ke da shi ga wasu a kasar tamu, wanda tabbas za a iya samun masu bukatar irin wannan tsarin a kasashensu. Ga shi ni ma duk da matsayin farfesa da na kai amma matsayi guda kawai hakan ke iya wakilta.

Shin, me ya sa mutum ba ya taba iya zama ba tare da wata damuwa ko wata bukata cikin zuciyarsa ba? Me ya sa mutum ke iya jinginar gona amma sai ya kasa noma ta? Ko wanda ya iya nomawa ya kasa girbewa, wanda ya girbe ya cashe ya kasa surfawa, ko a iya surfawa, a kuma iya dafawa amma a kasa taunawa? Me ya sa mutum ba ya taba zama kwararren da zai iya gamsar da kansa a komai ba?

Amsar ita ce mutum ba shi ya yi kansa ba, ba kuma shi ke tasarrafi da rayuwarsa ba. Wanda Ya yi shi Shi ya san yadda ya tsara al’amuransa don alaka tsakaninsa da ‘yan uwansa ta kyautata. Shi ne Allah Mai kaga mutum Ya kuma sarrafa tasirin al’amuransa. Tsarki ya tabbata gare Shi. Aminci kuma ga manzonSa.

Kuma na fahimci hakan, fahimta ta goguwa dake samar da ilimi ba ta karatu wanda ke samar da shaidar an yi ba.

No comments:

Post a Comment